Skip to main content

Yadda ake rooting din android.

Kafin kasan ya ake rooting kamata yayi kasan menene rooting kaji ana cewa nayi rooting ko zan rooting kai ma kake sanyi? Ko kuwa kaga ana maganrsa a dandalin internet ne ? Rooting wata hanyace ta karawa wayoyi ko tablet din android karfin aiki wato ka samu damar sa wasu application da Suke San suga an Samar da wani Abu da ake cewa super user binary ana sashi da alamu #superuser ko #superSU wannan hanya Tana sa guarantee da kamfanonin wayar suke ya wargatse har takansa waya lalacewa Amma amfaninta yafi hatsarinta yawa. In ba a bI hanyar yi dai-dai ba amma in anbi hanyoyin za aji dadin aikin.

Mene rooting?
Rooting kamar jailbreak ne a iPhone ga Wanda yayi amfani da wayar iPhone a da kuma Yana Ba masu amfani da waya damar chanja waya ainihin kwakwalwarta, hasali ma Yana bada damar chanja komai na waya zuwa yadda ake so. Da rooting zaka tsallake duk wani shinge da kamfanin da suka kera wayarka suka Sama Dan ragewa wayarka dadin amfani. Zaka sa applications masu matukar yawa da amfani,rage ko kara saurin wayar kai hatta da shi android din zaka iya sa sabon da Google suka Saki ko kamaYar da shi karami Wanda kake so ma'ana kana da yanci akan wayarka.

Saboda me Zakai rooting?

Abinda yake sawa ana rooting shine Google sun fito da sabon Android wato an kara wasu abubuwa kai kuma wayarka basu da wannan kana San sawa wayarka Amma kamfanin bai fitar Ba Sai wasu da ake kira developers ne sukai kamar irinsu CyanogenMod wadan da ake kira da Flash ROMs, Ko kuma an samo wata hanya ta saukaka browsing ance Sai anyi rooting kai Kuma wayarka babu. Irinsu browsing da MTN da subscription din blackberry ko na Glo.SU kuma applications sin ance Sai anyi rooting. Amma akwai applications da suke da dadi sosai da zasu sa kai rooting irinsu titanium Wanda zaka ajiye wayarka a memory dinka da sauransu.

Saboda me zaka ki yin rooting?

Abu biyu da zasu saka ka Ki rooting shine ka cire guarantee din wayarka ko kuma ka lalata wayarka a hanyar yi
Cire guarantee kamfanoni suna cewa in kai rooting ka cire  guarantee da suka saka Saboda duk wani shinge da suka saka ka tsallake shi Amma ka Sani in ka bukaci cire rooting zaka iya cirewa duk sanda ka so. Kaga wannan Ba matsala Ba ne.
Lalata waya. A kan samu tsautsayin lalacewar waya yayin rooting Amma Sai in Ba abi hanyar yin rooting din Dai Dai Ba in kabi hanya Dai Dai zakai cikin Nasara ka Gama Ba matsala Dan haka ka tabbata oa Bi hanyar da ta dace.

Abinda zakai kan kayi rooting.
Ana bukatar ka samu charge yakai a kalla kaso saba'in a cikin wayarka sannan ka tabbata kaje settings> developers options> USB debugging ka saka shi Kafin kai komai.

Yadda ake rooting.

Ana rooting ta hanyoyi guda biyu wato ta hanyar amfani da naura mai kwakwalwa da kuma hanyar da Ba amfani da naura mai kwakwalwa. Akwai applications guda biyu da suna da karfi da kyau wajan rooting Ba tare da computer Ba wato Ba na'ura mai kwakwalwa.
Framaroot da Towelroot Sai a computer akwai vroot da kingo root.

Towelroot

Hanya mai sauki da zakai rooting din wayarka ta android ahine towelroot zaka iya samun application din  a nan Amma Sai kaje settings>security>unknown source ka zaba sannan zai Shiga kamar Daya daga cikin application na wayrka Sai ka Shiga ka danna madanni Daya dake jikin fuskar application din zai kashe wayar yasake kunnanta Bayan ya Gama.



Framaroot

Kusan ko wace waya Framaroot na iya rooting dinta Ba tare da wahala Ba Sai Dai Yana da hanyoyi guda uku Wanda duk amfaninsu  daya Kawai in wani baimaka Ba Sai ka sake gwada wani akwai Barahin, Boromir da Faramir duk zasuyi Maka rooting sannan zai Baka sakon nasara sannan Sai ya tambayeka ka sake kunna wayarka Sai ka akshe ka kunna kasa rooting.
Hanya ta biyu wato amfani da computer Amma ita ma akwai hanya biyu akwai masuyin rooting babu internet akwai kuma wadanda Sai da internet kamar VRoot nayi babu internet Sai Kingo root da internet.

Vroot
Da farko zakai downloading vroot a internet Sai kasa ta cikin computer Bayan ka Gama ka kunna ta Sai ka jona wayarka da USB cable zata fara checking har zuwa tasa Maka sunan wayarka da model dinta, sannan zai Baka madannin root Sai ka JIRA zuwa ya Gama ya Baka sakon Nasara. Zai sake kashe wayar sannan zata kama da kanta ka samu rooting Kenan.

Kingo root
Bayan kayi download din application din kingo root Sai ka kunna internet dinka a computer taka ka jona wayarka zuwa computer Sai ka Jira har Sai wayarka ta ganu a jikin computer sannan Sai ka dannan madannin root dake jiki zai yi zuwa ya Gama.

Bayan kayi Daya daga cikin wadannan hanyoyi akwai hanya da ake gane aiki yayi ko bebe Dan wani lokacin basa saka superSU application a waya Sai kai download dinsa daga playstore zaka saka root checker a wayarka zata gayama kayi rooting ko bakai ba.

Amma duk da amfani da wannan rooting yake bayarwa wani lokacin akan so a cire shi to uanyar cirewa shine kaje cikin superSU dinka ka danna madannin remove root zai fita.

Comments

Popular posts from this blog

Wana irin waya ya dace ka siya?

Wana irin waya ya dace ka siya wannan amsar tana cikin me zakayi da wayar, mukan Sami matsala wajan siyan waya bamu san me zamuyi da ita ba Ko kuma wana irin sabon abu tazo da shi ba a'a kawai mai tsada ce to tana da kyau. Ba haka bane akwai Karin kudi na sunan kamfanin waya, domin zaka samu waya ta kamfanin Samsung da ta kamfanin HTC sunfi kowane kamfani tsada bayan akwai kamfanunuwa wadanda suke wayoyi masu kyau da sauki irinsu xiami, plus1, infinix da sauransu. Mun gwammace mu Sai mai tsadar nan kawai Dan ace na rike waya mai tsada. Akwai Abubuwa masu amfani guda biyar da su suka fi komai amfani a waya wato RAM, PROCESSOR, GRAPHICS,CAMERA Sai kuma Operating system wani lokacin internal storage. RAM. RAM ana kiransa da random access memory wato memory ne da yake Shiga ko ina dan ganin waya ta tafi dai dai, kuma yana da matukar amfani a cikinta domin shine yake bayyana me waya take da karfin yi, me zata iya dauka na application domin akwai game da zaka ga nauyinsu kadai y...
Yadda ake cire pattern ko password a Android. Kusan kowane mai wayar android ya Fama da matsalar pattern na ajiye waya wani yazo yayi ta gwadawa har Sai ya kulle wayan kaje an Maka flashing zaka koyi flashing din yanzu kaima kai wa kanKa Ba Sai Ka kashe kudi Ba. Yadda ake yi shine zaka kashe wayan ta Mutu wadda aka sawa pattern din aka rufe saika danne madannin kunnawa hade da madanni sauti da ake karawa Amma wasU wayoyin Sai Ka danne rage sauti wasU kuma Sai Ka hada ukun wato madannin kunnawa da na sauti ragewa da karawa zata kama kuma zata Dan yi vibration Sai kajira zata kai Ka waje kamar haka In kaga wannan ya fito Sai Ka daga zakai amfani da maddanan sauti wajan zuwa kan abiMnda kake so wato factory reset Sai Ka danna makunnin wayar zai kai Ka inda zaka danna kasa har Ka zabi yes  Bayan Ka zabi yes makunnin wayar zai dinga tafiya Yana rubuce rubuce har Sai ya Gama yasa ma wannan complete wato ya gama sai Ka danna wannan da makunnin wayar  Zata sake k...